Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Babachir Lawal, ya ce shi da wasu jiga-jigan siyasa masu goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour, Peter Obi, za su koma Kamaru idan dan takarar ya fadi zaben shugaban kasa a 2023.
Tsohon SGF ?in ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin wata tattauna wa da Obi da masu ruwa da tsaki na LP daga Arewa maso Gabas a Abuja.
Lawal, jigo a jamiyyar APC mai mulki, ya kuma bayyana mamakinsa da cewa APC ba ta kore shi daga jamiyyar ba, duk da adawar sa da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar, Bola Tinubu.
Ya kara da cewa zaben shugaban kasa na 2023 ya zama dole Obi ya lashe, idan aka yi laakari da halin da kasar nan ke ciki.
Ina cikin APC kuma mamba a kwamitin amintattu na jamiyyar, amma ina tafiyar Peter Obi/Yusuf Datti. Har yanzu APC ba ta kore ni ba. Ban san abin da suke jira ba.
Muna son (Obi) ya ci zaben nan kuma dole ne ya ci wannan zaben. Idan muka fadi wannan zabe, dukkanmu za mu yi hijira zuwa Kamaru saboda kunya da wulakanci na rashin cin nasara.

