Gwamnatin Tarayyar Najeriya ?ar?ashin jagorancin Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewar babu wani ?an Najeriya da zai tsallake daga yi mishi allurar rigakafin cutar nan mai sarke numfashi ta CORONA wadda aka fi sani da Covid 19.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar tuni dukkanin shirye shirye sun kankama na shigo alluran rigakafin domin fara aiwatar da yin su ga kafatanin jama’ar Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani dan kasar da zai tsallake wajen rarrabawa da kuma yin allurar rigakafin cutar corona a lokacin da rigakafin ya iso kasar.
Tuni bangaren zartarwa na gwamnati ta gabatar da kudirin Naira biliyan 400 a gaban Majalisar dokoki ta kasa da nufin sayen alluran rigakafin da za’a yi kyauta ga ‘yan Nijeriya.
Manyan ?asashen duniya da dama sun amince da fara aiwatar da yin allurar a kasashen nasu, tuni kasashe irin su Amurka da Faransa da kuma kasar Saudiyya suka rungumi wannan tsari na rigakafin cutar.
Cutar CORONA dai ta bayyana a duniya ne a ?arshen shekarar 2019 cikin watan Disamba, tun bayan bayyanar cutar ta hallaka mutane da dama a sassa daban daban na duniya, yayin da ta kwantar da miliyoyin jama’a.
Kasashen Duniya da dama sun ?auki matakan kariya ta hanyar ?a?aba dokar kulle ga jama’a, domin da?ile ya?uwar cutar tsakanin jama’a.
Cutar ta taimaka gaya wajen ?ara karya tattalin arzikin kasashen Duniya.
