Ministan shari’a Abubakar Malami yace sake fasalin nairar da Babban Bankin kasar yayi ya taimaka sosai wajen rage cin hanci da rashawa da kuma garkuwa da mutane domin karbar diyya a sassan kasar. Malami yace duk da ‘yan matsalolin da ake fuskanta da kuma sukar da wasu mutane keyi akan shirin, sake fasalin nairar ya taimaka sosai wajen shawo kan wasu matsalolin da suka addabi kasar.
Ministan yace an kaddamar da shirin sake fasalin ne domin taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ci gaba da yakin da yake yi a bangaren cin hanci da rashawa da kuma masu garkuwa da mutane dake mu’amala da takardun kudaden.
Yanzu dai haka wannan shiri na fuskantar babbar kalubale musamman ganin yadda ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin garari wajen hana walwala da kuma kasuwanci saboda rashin sabbin takardun kudaden.
Wannan ya sa wasu daga cikin gwamnoni da suka hada da Malam Nasir El Rufai da Yahya Bello da kuma Bello Matawalle rugawa kotun koli domin dakatar da shirin saboda irin matsalolin da ya haifar.
Shima gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotun kolin domin neman ta bayyana cewar bashi da hurumin aiwatar da shirin ba tare da mikawa majalisar ministoci da majalisar tattalin arziki sun amince da shi ba.
Masana tattalin arziki da dama na yabawa da shirin a bangare guda, yayin da suke kokawa akan lokacin da aka kayyade domin aiwatar da shi lura da irin rudanin da aka shiga a fadin kasar.
