Alhamdulillah Na Sauke Nauyin Da Na Dauka A Najeriya – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika manyan alkawura uku da ta yiwa mutane a 2015.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin bikin yaye daliban jami’ar tarayya dake Oye-Ekiti FUOY, a cewarsa, gwamnatin ta cika alkawarinta a bangaren tattalin arziki, rashin tsaro da kuma yaki da rashawa.

Buhari ya ce alkawarin da ya yiwa yan Najeriya shine zai inganta tattalin arziki, zai inganta tsaro kuma zai yi yaki da rashawa. Ya ce yana farin ciki saboda ya samu gagarumin nasara a wadannan bangarori guda uku.

“Bari in tuna muku na gina kamfe na a 2015 ne kan alkawarin inganta tsaro, karfafa tattalin arziki da yaki da rashawa.” “Ina godewa Allah cewa ina alfahari mun cika wadannan alkawura guda uku.”

“Lokacin rantsar da ni, kasar nan na karkashin mulkin yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro. Ina alfaharin cewa mun samu nasara kan yan ta’adda kuma mun kwato dukkan yankunan da suka mamaye.” “Hakazalika karkashin mulki na Najeriya ta farfado da tattalin arzikinta da ya kusan rushewa har zuwa yanzu da kasar ta zama mai tattalin arziki mafi girma a nahiyar Afrika.”

Related posts

Leave a Comment