Hukumar jiragen ?asa ta Najeriya, NRC, ta sanar da cewa za ta rage yawan zirga-zirgar jirage tsakanin Abuja zuwa Kaduna daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Oktoba.
Shugaban hukumar, Fidet Okhiria ya sanar da cewa za a yi hakan ne don gudanar da gyare-gyare.
Ya bayyana cewa a maimakon zirag-zirga sau goma a rana, za a yi guda hu?u ne kawai ranar 19 ga Oktoba da 20 ga Oktoba.
Ya ?ara da cewa ranar Alhamis 21 ga Oktoba kuwa, za a yi tafiya takwas ne.
Sanarwar tasa ta ce za a koma aiki yadda aka sana ranar Juma’a 22 ga Oktoba.
