Ba Za Mu Zuba Ido Muna Kallon Ana Karya Doka A Kasar Mali Ba – Buhari

Gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi tir da kama shugabannin Mali da sojojin ?asar suka yi, tana mai bayyana shi da “abin da ba za a amince da shi ba”.

Cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Waje, gwamnatin Najeriya ta ce kama Shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctar Ouane zai kawo tsaiko wajen mayar da ?asar kan turbar dimokura?iyya.

“Gwannatin Najeriya na kira da a saki shugaban ?asa da firaminista nan take ba tare da wani shara?i ba,” a cewar sanarwar.

“Wa?anda suka aikata wannan mummunan aikin su sani cewa ?asashe ?awayen Mali na Allah-wadai da tilasta wa shugabannin ko kuma matsa musu su sauka daga mulki.”

A jiya Litinin ne sojoji suka tsare shugaban Mali na ri?on ?warya da firaministansa jim ka?an bayan sanar da yun?urin kwaskwarima a majalisar ministocin ?asar, wanda zai sa a sauya manyan sojoji biyu da suka yi juyin mulki a bara.

Za a kori tsohon ministan tsaro Kanar Sadio Camara da kuma ministan harkokin soja Kanar Modibo Koné daga majalisar.

Related posts

Leave a Comment