Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Yan bindiga sun sake kai hari kasuwar garin Goronyo, karo na uku cikin mako biyu Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bu?e wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutane da dama.
Wata majiya daga garin ta bayyana cewa yan ta’addan sun kai hari da adadi mai yawa na mutane ranar Lahadi da daddare, inda suka bu?e wuta na kan mai uwa da wabi a tsakiyar jama’a a kasuwa.
Rahoton ya nuna cewa har zuwa yanzun ba’a san adadin yawan mutanen da harin ya shafa ba, amma mutane da dama sun mutu.
Wannan harin shine karo na uku cikin mako biyu da yan bindiga suka kai wata kasuwa a jihar Sokoto.
