Za A Gudanar Da Zabe Kamar Yadda Aka Tsara – Majalisar Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar majalisar tsaro ta ?asa da shugaban Buhari ya jagoranta ta bayyana cewa za a gudanar da za?en shugaban ?asa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, kamar yadda aka tsara.

Babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a na ?asar Abubakar Malamin ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ka?an bayan kammala taron majalisar a fadar shugaban ?asar.

Malami ya ce babban hafsan tsaro na ?asar Janar Lucky Irabor, da hafsoshin rundunonin sojin ?asar uku tare da babban sifeton ‘yan sandan ?asar sun yi wa majalisar bayani game da shirin da suka yi kan babban za?en da ke tafe ranar Asabar mai zuwa.

Ya ?ara da cewa ”dangane da haka, majalisar ta ha?u a kan cewa za?en na ranar Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara”.

Taron ya zo ne bayan, da taron majalisar magabata ta tabbatar da shirin hukumar za?en ?asar da na ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kan za?en na ranar Asabar mai zuwa.

Related posts

Leave a Comment