Sama Da Masu Yi Wa Kasa Hidima 200,000 Ne Za Su Yi Aikin Zabe – NYSC

Hukumar yi wa ?asa Hidima ta Najeriya (NYSC) ta ce ta tura masu yi wa ?asa hidima fiye da 200,000 da za su yi aiki a matsayin ma’aikatan wucin-gadi a za?en ?asar.

Daraktan hukumar Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai kan shirin da hukumar ta yi domin tunkarar baban za?en.

Janar Ahmed ya ce masu yi wa ?asa hidima su ne kusan kashi 75 cikin 100 na ma’aikatan wucin gadi a za?en da ke tafe.

Ya ?ara da cewa tuni jami’an hukumar za?en suka bayar da horo ga masu yi wa ?asa hidimar da za su yi aikin za?en.

“Masu yi wa ?asa hidimar a shirye suke domin gudanar da wannan gagarumin aiki, kamar yadda aka yi a baya, Tuni aka bayar da horo ga wa?anda za su gudanar da wannan aiki”.

Daga ?arshe Daraktan NYSCn ya garga?i masu yi wa ?asa hidimar kan kar?ar kyaututtuka daga hannun ‘yan siyasa.

Related posts

Leave a Comment