Tsohon ?an takarar Kujerar mataimakin Shugaban ?asa a jam’iyyar CPC a za?en 2011 Pastor Tunde Bakare, mai kulawa da cocin Citadel Global Community, ya musanta ikirarin cewa Buhari ya ci amanar ‘yan Najeriya a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana ra’ayinsa akan yadda Sunday Igboho ya shiga al’amarin kisan makiyaya, inda ya fito da bayanai dalla-dalla sa?anin yadda wasu Jaridu suka yi bayanan nashi bahaguwar fahimta.
Paston ya yi wannan musun ne a Arise TV, bayan an tambaye shi akan hirarsa da mawallafin Ovation Magazine, Dele Momodu, a Instagram.
Bakare ya musanta kalamansa, inda yace lallai ‘yan jarida sun kirkiri hakan ne don su samu jaridunsu su yi kasuwa.
“Gidajen jaridun sun kirkiri kalaman ne don su samu jaridunsu tayi kasuwa. Amma tabbas ban fadi hakan ba.”
“Hawan Buhari mulki a 2015 rahama ne ga mutane da dama. Duk da ana tsaka da rikici, fadace-fadace da sauran abubuwa, mutane sun cika sanya buri, wadanda da dama daga cikin burikansu basu cika ba.
“Lallai jaridu suna wallafa kalaman da za su janyo hankulan jama’a wurinsu ne. Amma maganar gaskiya, shin ya ci amanar ‘yan Najeriya?
Kullum muna ganin a labarai mutane suna bayyana takaicinsu da nadamarsu akan mulkin nan.
“Amma hakan ba ya nufin babu wani abin kirkin da wannan mulkin ya samar ba ne, tabbas akwai alhairai masu yawa da gwamnatin Buhari ta samar kuma a fili suke kowa na gani.
