Mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya baiyana cewa zai yi amfani da tarar N800,000 ?in da kotu ta yi wa gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
Ganduje dai ya kai ?arar Jaafar babbar kotu da ke Kano ne a 2018 bisa laifin ?ace da ?age bayan da fitaccen ?an jaridan ya wallafa wasu faya-fayan bideo da su ka nuna gwamnan ya na amsar dalolin Amurka a matsayin na goro.
To amma daga bisani, sai kotun ta yi umarnin Ganduje da ya biya Jaafar ?in N800,000 domin ?ata masa lokaci bayan da gwamnan ya janye ?arar.
A wata hira da Jaafar ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano a ranar Asabar, Jaafar ya baiyana cewa zai bayar da gaba ?aya ku?in ga shirin In da ran ka da ke ?auke da wani ?angare na neman taimakon lafiya da ku?in makaranta a gidan rediyon.
Jaafar ya ?ara da cewa zai cika N200,000 a kan ku?in su zama N1,000,000 domin a taimakawa masu ?aramin ?arfi.
A yanzu haka Jaafar ya samu mafaka a ?asar Ingila bayan da ya yi ?orafin cewa a na barazana ga rayuwarsa sakamakon fallasa faya-fayan dalar da ya yi.
