Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Kara Ba Shi Damar Ranto Bashin Tiriliyan Biyu

A daidai lokacin da darajar ku?in Najeriya ke ?ara ta?ar?arewar da har Dalar Amurka 1 ta kai Naira 550, a lokacin ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ke neman amincewar Majalisar Dattawa domin ya sake ciwo bashin dala biliyan 4 da kuma fam na Ingila 710.

Za a ciwo bashin ne daga wasu ?asashe da manyan cibiyoyin hada-hadar ku?a?e da bankunan duniya, domin a cike gi?in kasafin ku?in 2021.

Cikin wasi?ar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, ya shaida masu cewa bashin tun a kakar ku?a?e ta 2018-2020 ya ke a cikin tsarin bashi.

Buhari ya ce za a yi amfani da tulin basussukan domin ayyukan raya ?asa.

Ya ?ara da cewa za a tabbatar duk ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta amince za a yi har zuwa na amincewar cikin Yuni 2021, sun shiga cikin wa?anda za a aiwatar da ku?a?en basussukan.

Dala biliyan 4 dai a yanzu da Dala ke naira 550, daidai ku ke da Naira tiriliyan 2.2

Tulin Bashin Da Buhari Ke Ciwowa Ba Mai Kumbura Ciki Ba Ne -Gwamnatin Tarayya

Farkon watan Agusta ne Gwamnatin Tarayya ta ce tulin bashin da Najeriya ke ciwowa ba mai kumbura ciki ba ne.

Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed ta bayyana cewa har yanzu bashin da Najeriya ke ciwowa bai kumbura mata cikin da zai iya fashewa ba.

Ministar ta ce har yanzu Najeriya ba ta tsallake ?a’idar Gejin Tattalin Arzikin Cikin Gida na ba, inda ta ce har yanzu bashin bai wuce kashi 23 bisa 100 ba.

Zainab ta yi wannan bayani ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.

Cikin watan shekaranjiya ne Hukumar ?ididdigar Al?aluman Bayanai ta ?asa (NBS) ta bayyana malejin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) ya ?aru zuwa kashi 5.01 a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2021.

Zainab ta ce ai babu wani abin damuwa, domin ku?a?en da ake rantowa ana yin ayyukan raya ?asa ne da su, wa?anda su ka ha?a da aikin lantarki, titina, samar da ruwa da titinan jiragen ?asa, wa?anda su ne ?ashin bayan inganta tattalin arziki.

“Mu na ciwo bashi a cikin yin taka-tsantsan ?in da har yanzu ba mu wuce kashi 23 na Gejin Ma’aunin GDP ba.

“Na sha fa?a ba sau ?aya ko sau biyu ba cewa babbar matsalar ?asar nan ita ce ?arancin ku?a?en shiga, wa?anda ?arancin na su ke sa tilas a ke ciwo basussuka domin a yi ayyukan raya ?asa da inganta tattalin arzikin cikin gida.”

Kwanan baya ne Majalisar Tarayya ta damu da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ke ciwowa, alhali hukumomi ba su zuba ku?a?en shiga asusun Gwamnanti.

Kwamitin Lura da Ku?a?en Gwamnantin Tarayya na Majalisar Tarayya ya nuna ?acin rai ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.62 domin narkawa a yi ayyukan raya ?asa a kasafin 2021, amma kuma a gefe ?aya hukumomin Gwamnantin Tarayya da yawa sun ri?e ku?a?en shiga sun ?i zubawa a cikin Asusun Gwamnantin Tarayya domin a samu ku?a?en yin ayyuka.

Shugaban Kwamitin Ku?a?e na Majalisar Tarayya James Feleke ya ce, “a gaskiya ba mu jin da?in yadda wasu hukumomin gwamnati ke ri?e ku?a?e ba su zubawa cikin asusun Gwamnanti, ita kuma gwamnati an bar ta fita gaganiyar ciwo basussukan da za ta yi ayyukan raya ?asa.

“Don Allah ya zama wajibi mu tashi mu nuna kishin ?asar mu don mu ci moriyar bun?asar ta baki ?ayan mu.”

Feleke ya magana ne ganin yadda wasu hukumomin Gwamnantin Tarayya su ka kasa bada bayanai wasu kuma su ka ?i zuba ku?a?en shigar su a Asusun Gwamnantin Tarayya tsawon lokaci.

Kwamitin dai na gayyatar Hukumomi ne ?aya bayan ?aya su na gabatar da bayanan ku?a?en shigar da su ke tarawa duk shekara, domin a ji yadda za a yi kirdadon ku?a?en shigar da za su tara daga shekarar 2022 zuwa 2024.

Related posts

Leave a Comment