Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa ?an Najeriya da Angola za su fuskanci ?arin tsanani na hauhawar farashi da rashin wuta da rashin fetur da kuma ?arancin abinci.
Wa?annan matsaloli za su zo ne a yayin da farashin ?anyen fetur ya kai dala 120 duk ganga ?aya, lamarin da ake sa ran zai amfani wa?annan ?asashen da dama su ne manyan ?asashen Afirka da suka fi samar da fetur.
A wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar a ?arshen mako, ya ce “A ?asashen kudu da hamadar Sahara da dama, za a samu hauhawar farashi da da ?arancin wutar lantarki da ?arancin abinci da man fetur.”
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da dama Najeriya ke fuskantar matsannacin hauhawar farashi da ?arin samun layuka a gidajen mai a fa?in ?asar.
