BASHIR ADAMU, JALINGO
Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’ah Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS) ta Kasa ta Umurci Dukkanin Limaman Masallatan Juma’ah dana Idi a Najeriya da su fadakar da Al’ummah kan muhimmancin yin rijistan katin zabe.
Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Najeriya, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya shaida hakan a Birnin Jalingo fadan Jihar Taraba.
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo yace “ganin irin muhimmancin yin Katin zabe wato ‘Permanent Voters Card (PVC)’ ke da shi, da kuma irin yadda ake kukan cewa har yanzun nan akwai ‘yan kasa maza da mata da ba su yi rajistan wannan kati na zabe ba, ya zama wajibi su bada umurni ga dukkan Limaman Masallatan Juma’armu dana Idinmu na fadin Nigeria cewa su fadakar, su ja hankulan Al’umma cikin Hudubobinsu na Sallar Juma’a mai zuwa 2/12/1443 H, wanda zaizo dai-dai da /7/2022, da Sallar Idin Layya mai zuwa, a kan yin rajistar Katin zabe watau karban PVC”.
Kungiyar ta JIBWIS, na mai bayyana jin dadinta da sanarwar da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi na cewa za ta kara wa’adin yin rajistar zabe.
A cewar Dr. Jalo, “lallai yazama wajibi ga dukkan baliganmu su yi rajistan zabe a wannan zamani; domin Shari’a ta wajabta mana samar da Shugabanci na mulki, shi kuwa kaiwa ga Shugabanci na mulki a wannan zamani ba zai yiwu ba a garemu sai ta hanyar jefa kuri’a, shi kuwa jefa kuri’a ba zai yiwu ba sai in mutum ya yi rajistar katin zabe; abin da kuma wajibi ba zai cika ba sai da shi to shi ma ya zama wajibi; ke nan yin rajistar zabe ya zama wajibi a kan kowannenmu a Shari’ance”
A karshe, Shehin Malamin ya roki Ubangiji Allah da taimakon Sa har kullum, daya cigaba da taimakon bayinsa Musulmai, Amin.
