Yunwa Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Gurgunta ‘Yan Najeriya – Dino Melaye

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Dino Melaye ya yi wata wallafa ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram yana bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, kan hanyoyin da ya dace abi wajen saukaka wahalar rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Tsohon Sanatan ya bukaci shugaba Buhari ya yi gaggawar tallafa wa mutanen Najeriya sakamakon bakar yunwar da take addabar su, wadda ta yi musu dabaibayi ta hana su sukuni.

“Shugaba Buhari, ba lallai ka sani ba, akwai korafi da dama da ake yi a tituna. Mutane su na fama da yunwa, tsadar rayuwa ta na azabtar da talakawa. Ka yi wani abu kafin mutane su yi wani abu.”

Dama fitaccen dan siyasar ya saba da caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tun ba yau ba. Sanannen abu ne idan aka ce tsohon sanatan gwani ne wurin son wadaka da kuma hawa kasaitattun motoci kuma ya wallafa su a shafukan sa.

Da farko dai Dino Malaye ya hau kujerar sanata a jihar Kogi ta jam’iyyar PDP, daga bisani ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC, daga baya kuma ya kara komawa jam’iyyar PDP inda ya so ya zarce a kan kujerar sa a zaben 2019.

Abokin takararsa na jam’iyyar APC, Smart Adeyemi ya maka shi a kotu inda ya bayyana rashin gamsuwar sa dangane da zaben. Daga nan ne kotu ta umarci sake yin zaben wanda Smart ya yi masa mummunan kaye ya maye gurbin sa a kujerar sanatan.

Related posts

Leave a Comment