Halin Da Najeriya Ke Ciki Dambu Ne Ya Yi Yawa – Faruok Adamu Aliyu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Wani babban jigon jam’iyyar APC Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana cewa lallai sun jahilci halin da Najeriya ke ciki lokacin da suka yiwa yan Najeriya alkawarin canji a 2015.

Zaku tuna cewa a 2015, Jam’iyyar APC ta tsaya takarar zabe kuma ta kayar da gwamnatin PDP na shekaru 16 bisa alkawarin kawowa Najeriya canji.

Faruk Adamu Aliyu, wanda tsohon dan majalisa ne karkashin jam’iyyar ANPP ya ce rashin isasshen ilmi kan halin kasar yasa suka yiwa Najeriya wannan alkawari.

Ya bayyana hakan ne a shirin “Politics Today ” na tashar ChannelsTV ranar Alhamis. Yace alkawuran da suka yiwa yan Najeriya yasa jama’a suke ganin babu cigaba duk da dimbin ayyukan da gwamnatin Buhari ke yi a shekaru 6 da suka gabata.

“Bari in amince, lokacin da muke jam’iyyar hamayya, akwai wasu abubuwan da mukayi cikin jahilci, a kuma son rai.” “Lokacin mun zagaya jihohin Najeriya domin zanga-zangar cire tallafin mai. Lokacin mun jahilci abun, wannan shine gaskiya.”

“Yayinda muka dane kan kujerar mulki, sai muka fahimci Jonathan ba kuskure yayi ba, ya kamata a cire tallafi.” Faruk Adamu ya kara da cewa yanzu sun fahimci cewa Jonathan na kan hanya.

Related posts

Leave a Comment