Kungiyar Kare Muradin Yarabawa Zalla ta Afenifere, ?angaren shugabancin Ayo Adebanjo, ta bayyana cewa ta na goyon bayan fita a yi zanga-zanga kwanaki 10 da ake shirin farawa daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agusta.
Kakakin Ya?a Labaran Afenifere ?angaren Ayo Adebanjo, Falmata Daniel ne ya bayyana cewa za a fita zanga-zanga saboda yadda Shugaba Bola Tinubu ya ?ora tattalin arzikin Najeriya a kan hanyar da ba ta ?ullewa, sai dai ta jefa ?asar nan cikin masifar ra?a?in tsadar rayuwa.
Sakataren Ya?a Labarai na Afenifere, Justice Faloye ne ya bayyana haka.
“Afenifere ba ta shirin shiga zanga-zanga, amma fa muna goyon bayan duk wanda zai fito ya nuna damuwar sa kamar yadda ‘yancin ?an Adam ya ba shi damar fitowa ya yi.
“Saboda Afenifere ta sha garga?i kan makauniyar hanyar da wannan gwamnati ta ?ora tattalin arzikin ?asa. Idan ka ci gaba da cire tallafin fetur, kuma ta haifar da tsadar rayuwa, to ai kuwa babu yadda za a yi ka hana mutane fitowa. Ba za ka iya tausasa zukatan mayunwata ka ce wai su zauna a gida ba.” Inji Faloye.
Afenifere ?angaren Ayo Adebanjo sun ?alle daga Afenifere da ke ?ar?ashin Reuben Fasoranti daidai lokacin gabatowar za?en 2023, saboda su na goyon bayan ‘yan takarar shugaban ?asa daban-daban.
Yayin da ?angaren dattijo Fasoranti ke goyon bayan APC da ?an takarar ta Bola Tinubu, su kuma ?angaren Ayo Adebanjo sun goyi bayan jam’iyyar LP da ?an takarar ta Peter Obi.
Dattijo Adebanjo mai shekaru 96 a duniya, ya yi zargin cewa Fasoranti mai shekaru 98 a duniya nauyin shekaru sun yi masa yawa, saboda haka yanzu shi ne jagora.
Faloye a ranar Alhamis ya ce tun a baya sun sha garga?in gwamnatin Tinubu dangane da makahon tsarin tattalin arzikin da gwamnatin sa ta bijiro da shi, amma aka yi watsi da shawara da garga?in ?ungiyar. Sai gwamnati ta ce wai siyasa abin ba shawara ba.
