Nasararmu Ta Shekara 6 Ta Zarce Shekaru 16 Na PDP – APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC tace Najeriya ba zata koma ruwa ba ?arkashin mulkin PDP a shekarun baya, kuma tabbas Najeriya zata cigaba kamar yadda APC ta dorata a tsari.

Jam’iyya mai mulki ta APC ta fa?i hakane domin maida martani kan maganar tsohon mataimakin shugaban ?asa Atiku Abubakar kuma ?an takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na 2019.

A ranar Alhamis, bayan ganawa da Gwamna Wike na jihar Rivers, Atiku yace yan Najeriya Allah-Allah suke PDP ta dawo kan mulki a 2023, saboda abin da ya kira halin kunci da suke ciki.

Tsohon mataimakin shugaban ?asa, yace: “Na yi imani cewa yan Najeriya sun kosa 2023 ta zo saboda jam’iyyar PDP ta dawo kan madafun iko domin dawo da ‘yan kasar cikin gayyaci su”.

Na shekara sama da 70 a duniya amma ban ta?a ganin Najeriya ta lalace kamar yadda take yanzun ba, ta ?angaren kalubalen tsaro, rashin aikin yi, ban taba gani ba domin abun yayi muni sosai.”

Amma da yake martani kan maganar Atiku, Sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta ?asa, John Akpanudoedehe, yace Najeriya ba zata koma ruwa ba bayan tsamar da ita daga mulkin danniya na PDP da Allah ya yi.

“Ya kamata Atiku yasan cewa yan Najeriya ba zasu koma kasar Masar ba, ba zasu sake komawa ruwa su za?i PDP ba a 2023 bayan sun gwada sunga gazawarta.”. “Ta wane fannin ma zance babu wani abu mai kyau dake fitowa daga PDP, sun rike Najeriya na tsawon shekara 16 amma babu wata nasara da zasu iya nuna wa.”

“Nasarorin da jam’iyyar mu ta APC ta samu a ?asa da shekara 8 sun shafe mulkin da PDP ta yi na shekara 16. APC ba tsarar PDP bace ta kowane fanni.”

Related posts

Leave a Comment