Zanga-Zanga: Za Mu Canza Take Zuwa Ga Kiran Tinubu Ya Sauka Muddin Aka Taba Mu – Jagororin Zanga-Zanga

IMG 20240226 WA0252

Masu shirya zangazanga a Najeriya sun ce kashe mutanensu ko kamasu, ko kuma raunatasu a lokacin zanga-zangar, zainsa su bukaci shugaban Tinubu ya yi murabus,’ don haka suke gargadi ga hukumomin tsaro, suka ce ba za su ja da baya ba har sai Tinubu da dukkan ministocinsa sun sauka, muddin abubuwan da suka lissafo suka faru.

Jaridar The Gazzetta ta rawaito masu shirya zanga-zangar da suke wa take da #EndBadGovt a fadin kasar nan da ke tafe sun gargadi hukumomin tsaro cewa za a samu sakamako idan aka kai wa wani daga cikin masu zanga-zangar hari.

A cewar masu zanga-zangar, za su bukaci shugaba Bola Tinubu da daukacin majalisar ministocinsa da su yi murabus, idan an kai wa daya daga cikinsu hari a ko wani yanki na kasar.

Jami’an tsaron sun yi gargadin kan mace-mace da barnar da masu zangazanga suka yi sanadiyyar zanga-zangar #EndSARS a watan Oktoban 2020, da kuma tashe tashen hankulan a baya bayan nan a Kenya, tare da nuna damuwa cewa zanga-zangar #EndBadGovt na iya faruwa cikin yanayi mara da?i.

Sai dai a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo, masu tallata zanga-zangar da ke tafe wacce ke dauke da ajandar guda 10, wadanda suka shirya zanga-zangar, su kuma suka gargadi ga jami’an tsaro da cewa, “A yayin wannan zanga-zangar, idan aka kashe mutum daya ko aka raunata ko aka kama shi, “ba za mu ja da baya ba, har sai Tinubu da daukacin majalisar ministocinsa sun sauka daga mulki.” a cewarsu.

Duk da barazana da ikirarin da jami’an gwamnati suka yi na cewa sojojin haya na kasashen waje ne suka dauki nauyin zanga-zangar, masu shirya zanga-zangar sun yanke shawarar ci gaba da zanga-zangar a ranar 1 ga Agusta, 2024.

A cewar masu shirya zanga-zangar adawa da yunwa da wahalhalun da ake fama da su a kasar nan ne sakamakon munanan manufofin tattalin arziki na shugaba Bola Tinubu tun hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Related posts

Leave a Comment