Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa an bayyana sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa na jamiyyar APC a zaben 2023.
Lamarin na zuwa ne ‘yan awanni bayan Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na kujerar, ya jadadda cewa ba zai janyewa shugaban majalisar dattawan ba.
Lawan dai ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jamiyyar APC sannan awanni kafin fara zaben fidda gwanin sai shugaban jamiyyar na kasa, Abdullahi Adamu ya sanar da shi a matsayin dan takarar maslaha na jamiyyar.
Daga baya Sanatan ya sha ?asa a hannun jagoran APC na Kasa Bola Tinubu wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.

