Wani ?an kasuwa mazaunin unguwar Agadasawa a Kano, Alhaji Ibrahim ya yi wa ?iyar makwabcinsa ciki, mai suna Humaira Hussaini ?ar aji uku a ?aramar Sakandare (JSS3).
Mujallar Neptune Prime ta ruwaito zantawarta da yarinyar Humaira Hussaini a Kanon kuma ta shaida mata yanda lamarin ya faru da cewa: “Alhaji Ibrahim ya kira ni zuwa gidansa wata rana bisa dalilin cewa yana son ya aike ni amma lokacin da na shiga gidan, sai na gano iyalinsa ba sa gida. Ya kulle ?ofar gida ya ba ni lemon sha kuma ya yi barazanar cewa idan ban sha ba, zai kashe ni.
“Na kar?i lemon, bayan na shanye sai kasala ta kamani shi kuma Alhaji Ibrahim ya yi min fya?e”.
Humaira ta ?ara da cewa tun daga wannan lokacin, sau ?aya kawai ta ga jinin al’adar ta, kuma bayan wasu watanni ta sanar da mahaifinta, Hussaini Ado abin da ke faruwa shi kuwa ya kai ta asibiti. A asibitin, aka umarci mahaifin nata da ya je ya shirya kayan haihuwa domin ta fara na?uda tana gab da haihuwa.
Mahaifiyar yarinyar, Hajiya Rafa’atu Hussaini ta shaida wa majiyar mu cewa ba ta taba zargin cewa ‘yarta na ?auke da juna biyu ba har sai da ta haifi jaririn, kuma ta tabbatar musu da cewa makwabcinsu, Alhaji Ibrahim ne ya yi mata.
Sai dai a lokacin da aka tinkari Alhaji Ibrahim da wannan batu, ya nemi da aje a yi gwajin ?wayar halitta na DNA, wanda bayan an yi likitan ya tabbatar da cewa lallai jaririn nasa ne amma bai yadda ba ya sake neman a sake zuwa wani asibitin a yi.
Tuni dai aka shigar da ?ara ofishin ?an sanda amma har yanzu iyayen yarinyar sun sanar da kasa gane inda lamarin ya dosa domin suna zargin ?an kasuwan na so ya yi amfani da dukiyarsa wajen shashantar da shari’ar.
Iyayen Humaira sun nemi agajin ?ungiyoyin Kare Ha??in Biladama da ?ungiyoyi masu zaman kansu da hukumar Hisba ta Kano da Lauyoyi da ?an jaridu da su shiga cikin wannan lamari.
