Adamawa: An Bukaci Gwamnatoci Su Samar Da Shirin Taimakon Kananan ‘Yan Kasuwa

An kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su kirkiro shirin da zai tamakawa yan kasuwa musammanma kananan yan kasuwa a fadin kasan nan baki daya.

Shugaban yan kasuwa na aewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar yanci a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Muhammed Ibrahim yace taimakawa yan kasuwa yana da mutukan muhimmanci domin a cewars za a samu cigaban kasuwanci dama samar da aikinyi a tsakanin matasa tare da samar da zaman lafiya a kasa baki daya.

Ibrahim 86 ya kuma yaba da yadda gwamnatin tarayya ta bullo da wasu tsare tsare daban daban domin ganin an samu cigaban samar da sanà ar dogaro da kai musammanma a tsakanin matasa.

Da wannan yake shawartan gwamnatocin jihohi da suma subi sahun gwamnatin tarayya na kirkiro tsare tsare daban daban. a hihohinsu wanda hakan zai taimakawa kananan yan kasuwa dama matasa wajen dogaro da Kansu.

Ya kuma kirayi yan kasuwa da sukasance masu hada Kansu waje guda da kuma baiwa shuwagabannin kungiyartasu hadin kai da goyon baya wanda acewarsa haka zai kawo cigaban kungiyar yan kasuwan yadda ya kamata.

Tare da shawartarsu da su ksance masu bin doka da oda a koda yaushe domin samun zaman lafiya a tsakanin yayan kungiya dama kasa baki daya.

Harwayau ya kirayi yan Najeriya da su kasance masu gudanar da aiyukan cigaban kasa dà kuma baiwa Jami an tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin an kawo dukkanin kalu balen tsaro a fadin kasar baki daya.

Related posts

Leave a Comment