Shirin Ciyar Da Yara A Makarantu Barnar Kudi Ne – Ilallah

Layin da shugabanni suka shata tsakanin su da talakawa, ke sanya su kawo baragruban tsare-tsare a cikin harkar ilimi, su kuma kauda kai a zahirin matsalolin al’ummah, domin su yaransu basa zuwa makarantun gwamnati, wannan ya sanya harkar mulki ta zama siyasa ba amana ba. Damar da Demokadiya ta bayar na zaben su, ya zame musu hanyar arzurta kai da neman dawwama a kan mulkin al’ummah.

Shin ko yaushe shugabanni zasu riki al’amuran jama’arsu da mushinmanci? Ko yaushe ne “Yan Nijeriya zasu fuskanci zahiri akan matsalolin su, su kuma fuskanci zahiri hanyoyi na maganin matsalolinsu, musanma ma a kan harkar ilimi, wanda a kullum tsarin ilimin Nijeriya musamman ma arewacin kasar koma baya yake samu.

Tabbas, tulin matsalolin ilimi a Nijeriya daga sama har kasa, ya zamanto abin tashin hankali da takaici. Wannan matsalolin sun bada gudunmawa mai tsoka wajen koma bayan Nijeriya, yawaitar rashin tsaro, rashin aikin yi, da kuma tsananin talauchin da al’umma ke ciki.
Rashin kyawawan manufofi da tsare-tsare masu kyau na shugabbanni, musamman wajen yadda ya dace wajen sanya kudaden a harkar ilimin ya jawo lalata Biliyoyin kudaden ‘Yan Nijeriya, sannan ya sake sanya tsarin ilimin cikin rudani.

Tabbas, duk tsarin da akayi, ko manufa na inganta ilimi, in har aka gaza samar kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa, ingantattun Malamai, kyakkyawan jadawali na koyarwa, baza a iya cimma buri da manufar ilimi a Nijeriya, musamman yain da al’ummah ke cikin tsananin rashin tsaro da kwanciyar hankali.

Ilimin Firamare shi yafi kowanne shiga bala’I da tasku, musamman ma a arewacin Nijeriya. A kwai makarantun firamare da in ruwan sama ya zo, to karatu yakare saboda, saboda su kansu ajujuwan cika suke da ruwan sama, a wasu jahohin babu isassun Malaman-Makarantar, wasu makarauntun ma, Malami daya ne tak. A ma kusan dukkanin makarantun a kwai tsananin rashin kujeru da teburan zama, yara saidai su zauna a kasa domin yin karatun.

Baban tashin hankali a wannan zamanin, shine kin fadawa kanmu gaskiya, koda kuwa an san gaskiyar ce.

Babban ganganci shugabannin wannan zamanai shine kawo tsari da bashi da inganci, ko kwaikwayon tsarin wasu kasashe ba tare da nazarin yanayin kasarmu ba, wasu lokutan tsarin da aka kawo yakan rusa ingancin sa bisa dalilai na aiwatar dashi ko tsarin ya yi karo da wani ibtila’I da zai rusa ingancinsa. Wani lokacin a kawo tsari da ba mai dorewa, kuma a cigaba da barnatar da kudin al’ummah, ana sane, ba tare da an gyara ba.

A wani lokutan masu mulki kan kawo tsari, mai mutakar muhimmanci kamar wannan tsarin na ci da yara yan makaranta da abinci, amma aiwatar da shi kan rusa ingancinsa. Cin-Hanci da Rashawa, kutse da kan faru bagatatan, misali hauhawar firashi (inflation), karuwar talauci, afkowar annoba misali kamar Corona, wadannan dama wasu ya yiwa wannan tsarin tasgaro, kuma yayi masa tarnaki wajen samun inganci, ko ma ya biya bukatar manufar shirin, duk da dubban miliyoyin al’umma da ake kashewa.

Tun asali ma su kansu shugabanni sun san shirin ba mai daurewa, kuma kwalliya bazata biya kudin sabulu ba, duba da yanayin tafiyar tattalin arzikin Nijeriya.

A nawa nazarin gwamnatin Buhari ta kashe magudan kudi har Naira Biliyan Biyar da Miliyan Dari da Saba’in da Bakwai (N5.178B) a tsakanin 2017 – 2020 a watan Augusta a Jahar Jigawa kadai, wajen ciyar da dalibai abinci.

Abin takaicin, muna ganin irin abincin da ake bayarwa wanda bai wuci ludayi daya ba.

Tambaya anan shine: Don Allah Ludayi daya da ake ba wa yaro/yarinya wanda bai wuci loma uku ba, shine zai ishi yaro, har ya samu karkashin yin karatu? A wannan asabar din da ta gabata, naje wata makarantar firamare ta islamiya, naga an rabawa yara dalibai ruwa kwalli daya (Pure Water) a madadin abincin wannan ranar, abin dariya amma kuma abin takaici da tashin hanakali.

Kowa ya sani da Shugabannin, Iyayen Daliban dama Daliban irin yadda ake raba abincin nan. Ko wa yake yaudarar wani tsakanin shgabannin da al’ummah?

Da dama daga cikin makarantun firamaren nan basu da kujeru na zama, wata makarantar ma Malami daya ne, wata biyu, duka da jahar na fama da rashin ingancin koyarwa.

In har gwamnati tarayya na da niyar tallafawa ilimin, me yasa baza a kalli zahirin matsaloli ba wanda suke hakki ne gwamnati don sauke su.

Shin wai lokaci baiyiba da kowa zai dauki nauyin da ke kansa wajen ilimantar da yaran mu ba?

Ya kamata iyaye su sauke hakkin da ke kansu wajen ciyar da yaransu, ita kuma gwamnati ta samar da kyakkywan yanayi na koyo da koyar wa. Ta haka ne kowa zai sauke amanar take kansa.

Hatta a shekarar da ta gabata, a lokacin da akayi lockdown saboda annobar Corona akwai jita-jita na cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe N13.5 Billion do ciyar da yara ‘Yan-Makaranta, amma daga baya Ministar Walwala Hon. Sadiya Farouk ta musanta, yayin da ta tabbatar da kashe N523.3 Miliyan kawai yayin da ake kulle a fadin Nijeriya. Baban takaicin mun kasa neman ba’asi yadda ake kasha kudin al’ummah, hatta wakilan mu a zauren majalissar dokoki, duk da mun san abin da kamar wuya.

Lokaci yayi da masu ruwa da tsaki za suyi duba na adalci akan harkar ilimi musamman a na arewacin Nijeriya da suke koma baya.

alhajilallah@gmail.com

Related posts

Leave a Comment