Za A Sha Mamaki Idan Na Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci – Bawa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan Najeriya za su sha mamaki matuka a lokacin da zai fallasa sunayen masu ?aukar nauyin ta’addanci a kasar.

Abdulrasheed Bawa ya ?ara da cewar jama’ar kasar za su san sunayen masu ?aukar nauyin ta’addanci a lokacin da ya dace, na bada dadewa ba cikin yardar Allah.

Shugaban Hukumar EFCC din yana magana ne yayin wani shirin siyasa na tashar talabijin ta Channels ranar Alhamis.

Bawa, wanda ya fadi lokacin da yake jawabi a fadar shugaban kasar a ranar, ya ce likitoci sun shaida masa cewa bashi da wata matsala, don haka a yanzu ya murmure.

”Makoshi na ne ya dan bushe, sai likitoci suka bukaci in sha ruwa sosai, daga baya kuma na wartsake ba wata matsala yanzu” inji shi.

‘Yan Najeriya dai sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da faduwar da Shugaban hukumar EFCC yayi a yayin gabatar da jawabi, inda ra’ayoyin ‘yan ?asar ya bambanta da juna.

Related posts

Leave a Comment