‘Yan Siyasa Ne Suka Gurbata Malamai – Dr Gumi

Mashahurin Malamin Malamin addinin Islaman nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya yi Alla-wadai da yadda yan siyasa sukayi tururuwa zuwa daurin auren ‘dan Buhari da Zahra Bayero.

Babban Malamin ya yi Alla-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al’umma wajen baja koli da hayar jiragen alfarma.

Malamin ya yi bayyana dalilin da yasa Malamai ba sa iya fadawa shugabanni gaskiya. Yace duk yan siyasa sun lalata Malaman addini shiyasa basu iya musu wa’azi, su fada musu gaskiya.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya bayyana hakan ne yayin gabatar karatun mako-mako da yake gudanarwa a Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna.

“Kar ku ba Malamai laifi, domin wani Malamin ba zai iya rayuwa sai yayi dan amshin shata saboda yunwa. Wani Malami in yayi wata magana ba zai kwana gidansa ba, cikin Cell zai kwana.

In kuma an nemeshi zaku je ku fito da shi? Dole yayi shiru.” “Shiyasa Yan siyasa suka lalata mana Malamai. ana barna cikin kasa ba mai wa’azi, ba mai gaya musu gaskiya. Sannan barnan nan babu inda za ta kaimu sai ga wahala.”

Related posts

Leave a Comment