Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje a ranar Asabar, ya mika sandar girma ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero, a matsayin Sarkin Bichi na biyu.
Masarautar ta Bichi tana daya daga cikin sabbin masarautun da gwamnatin Ganduje ta kirkiro, a shekarar da ta gabata. Sauran sabbin masarautun da aka kirkiro sune Rano, Gaya da Karaye, baya ga majalisar masarautar Kano da ake da ita.
Da yake jawabi bayan gabatar da sandar girma ga sarkin, Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta yaba da gudummawar da masaratun ke bayarwa don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ganduje ya ce gudummawar da sarautar gargajiya suka bayar, ya sanya gwamnati ta kirkiro karin masarautun, da nufin fadada ci gaba zuwa yankunan da ke kasa.
Ya bukaci Sarkin da sauran sarakunan jihar, da su ci gaba da ba gwamnati gudunmawa wajen samar da tsaro ga dukiyoyi da rayukan jama’a. Gwamnan ya bukaci Sarkin da ya ci gaba da zama uba ga duk talakawansa ba tare da nuna bambanci ba.
A jawabinsa na mika godiya, sabon Sarkin na Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yayi alkawarin yin adalci ga dukkan mutanen masarautar.
Ado-Bayero ya bukaci mutanen masarautar da su kara himma wajen shigar da yaransu cikin tsarin ilimi na asali.
