Jam’iyyar PDP ta sake tuma tsalle ta haye kan Shugaba Muhammadu, ta na caccakar sa, dangane da sabon al?awarin da ya sake ?auka cewa zai kawar da matsalar tsaro kafin ?arshen mulkin sa a 2023.
A ranar Alhamis ce aka ruwaito Shugaba Buhari ya sha alwashin kawar da matsalar tsaro kafin ?arshen mulkin sa cikin 2023.
Ya yi wannan furucin ne ta bakin Mashawarci Na Musamman kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, inda ya ce Buhari ya ce “ba zai bar mulki a matsayin wanda ya kasa ba.”
Matsalar ‘yan bindiga na ci gaba da tsamari a Yankin Arewa Maso Gabas da ya ha?a da Katsina mahaifar Shugaba Buhari, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Ko a ranar Alhamis da dare ‘yan bindiga sun tasa ?eyar mutum 60 a ?auyen Rini, cikin ?aramar Hukumar Bakura, ta Jihar Zamfara.
Akwai ?aruruwan jama’a ciki har da ?alibai sama da 200 yanzu haka a hannun ‘yan bindiga.
Har yanzu ana ta ja-in-ja dangane da ku?in fanso mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara da kawunnan sa uku da kishiyar mahaifiyar sa, wa?anda ke hannun ‘yan bindiga tsawon makonni uku.
Yayin da PDP ke mayar da raddi ga Buhari, ta bayyana cewa Buhari bai yi wani abin kirki da zai iya gamsar da mutane cewa zai iya cika al?awurran da ya ?auka tun kafin ma ya hau mulki ba.
A kan haka PDP ta ce Buhari ya lalata ?asar nan, kuma haka zai sauka ya bar ta a lalace, fiye da yadda ya kar?i mulkin ?asar cikin 2015.
Kola Ologbondiyan wanda shi ne Kakakin Ya?a Labarai na PDP, ya ce ?o?arin da Buhari ke yi na gyaran matsalolin Najeriya, ci gaban mai ha?ar rijiya kawai ya ke yi. Kuma APC tuni ta lalace, ta ?al?alce, ta zama ba abin dogaro wajen ceto Najeriya ba.
Kola ya ce Shugaba Buhari da APC sun kasa wajen al?awarin su uku na ya?i da rashawa, samar da tsaro da kuma inganta tattalin arzikin ?asa.
“Wane bugun ?irji Buhari da Gwamnatin APC za su yi a lokacin da ‘yan bindiga ke kwashe mutanen da hana su kwana gidajen su har wasu na gudun hijira!
“Ina tsaro idan aka dubi yadda ‘yan ta’adda ke karkashe jama’a a ?asar nan?”
PDP ta yi wa Buhari gori cewa hatta jihar sa ta haihuwa ba ta ta?a shiga cikin tashin hankali ba, kamar a zamanin mulkin sa.
