Kano: Ruftawar Gini Ya Hallaka Yara Uku A Dakin Mahaifiyarsu

Rahoton da muke samu daga Jihar Kano na bayyana cewa wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Tarai na karamar hukumar Kibiya bayan rushewar wani gini da ya yi sanadin rasuwar yara uku ‘yan gida daya a ?akin Mahaifiyarsu.

Mahaifin yaran da suka rasun, Abubakar Usman ya shaidawa babban sakataren SEMA, Saleh Jili lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa ta’aziyya a garin yadda abin alhinin ya kasance.

Ya ce wadanda suka rasun sune Umar Abubakar, Aliyu Abubakar da yar uwarsu Aisha Abubakar, sakamakon fa?owar da gini ya yi musu suna cikin bacci.

A cewar mahaifin, yaran ‘yan shekara hudu, biyar da bakwai sun rasu ranar Lahadi 7 ga watan Agusta lokacin da ginin dakin mahaifiyarsu ya rufta saboda ruwan sama da aka yi na kwana biyu. Ya ce: “Wani dan uwa na ya kira ni ya sanar da ni cewa ya’ya na uku sun rasu domin na yi tafiya zuwa kasuwanci.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, Saleh Jili, wanda ya jagoranci tawagar zuwa Kibiya ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi bakin cikin samun labarin mutuwar yaran inda ya mi?a ta’aziya ga iyayen yaran.

Ya ce hukumar zata tattara rahoto ta ba gwamnati don a dauki mataki. Jili ya ce hukuma ta samar da katifu, matashi da kayan abinci da na gini ga iyalan wadanda suka rasun.

“Muna bada shawara a daina gini kan hanyar ruwa,” in ji shi. Hakimin Kibiya kuma Sarkin Shanun Rano, Alhaji Abubakar Ila, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Related posts

Leave a Comment