Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa ba zai ri?a zuwa Kaduna ba har sai in ya zama dole bayan kammala wa’adin mulkinsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Abuja, a wajen taron ?addamar da wani littafi a ranar Talata. El-Rufai’n ya ce ba zai amshi kujerar Ministan Birnin Tarayya ba koda an bashi.
Sai dai gwamnan bai bayyana cewa ko zai zamo ?aya daga cikin wa?anda za a tafi da su a wannan gwamnati ko a’a ba, illa iyaka dai ya bayyana cewa ba zai kar?i kujerar ministan Abuja ba.
El-Rufai dai ya kasance shine tsohon ministan Abuja a lokacin tsohon shugaban ?asar Najeriya, Olusegun Obasanjo, wanda a lokacinsa an yi gagaruman ayyuka, ciki kuwa hadda rushe-rushen manyan gurare a Abuja.
“Na gama aiki na, na gama, bana waigawa baya. Tun da na bar birnin tarayya ban ?ara komawa ba sai a shekarar 2016, lokacin da aka bawa wani ?an ajinmu a sakandire mu?amin minista.” “Duk wani mu?ami da na bari, ba na sake waiwayar shi, idan na bar Kaduna nan da kwanaki 19, ba zan ri?a ma zuwa ba sai in ya zama dole.”
El-Rufai ya ?ara da cewa: “Koda an bani mu?amin, to ba zan kar?a ba in tafi Abuja ba. Kamar yadda nace, ba na maimaita aji, kuma nasan matasa masu ?anyan jini da zan iya turowa su yi aikin fiye da yadda na yi a lokacin ina ministan.” “Shekaru na sun yi ma mu?amin yawa. Yanzu na girmi yin rusau, a samu matashi mai jini a jika ko matashiya a bata mu?amin.”
