‘Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Hallaka Ganduje A Zamfara

Lamarin ya farune a tsakanin garin Shema da Funtua na jihar Katsina, inda jami’an tsaron sake tawagar gwamnan suka yi musayar wuta da ‘yan Bindigar.

Tawagar motocin na dawowa ne daga karbar Gwamnan Zamfara da ya koma APC.

Saidai a yayin da lamarin ya faru Gwamna Ganduje baya cikin tawagar motocin, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.

Wajan dawowa, Gwamna Ganduje ya bi tawagar motocin Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru inda suka koma tare. Dalilin hakan kuwa shine tawagar motocinsa basu sha man da zai koma dasu Kano ba, wanda hakan ya batawa gwamnan rai kamar yanda majiyar ta bayyana.

Saidai harin bai yi nasara ba, domin jamu’an tsaron dake tare da tawagar sun dakileshi. Saidai ‘yansanda 2 sun jikkata a yayin da kuma motar daukar marasa lafiya dake tare da tawagar ta samu harbe-harben Bindiga.

Hakanan tayar daya daga cikin motocin ma ta fashe bayan da harsashi ya sameta.

Related posts

Leave a Comment