A ranar Talata ne 29 ga watan mayu na shekarar 2021 sananen matashin dan’Jarida kuma mawallafin Wikki Times akan yanar gizo a Jihar Bauchi Haruma Mohammed ya shaida ma manema labarai cewa rayuwarsa tana cikin hadari da dar-dar a dalilin wasu matasa da suke farautarsa,
Yace hakan baya rasa nasaba da wani rahoto da ya wallafa kan badakalar kudi na aikin dan Majalisa Yakubu Dogara, a yankin da yake wakilta, kuma tsohon kakin majalisar tarayya ta kasa
Rahoton da shi wan nan dan’Jarida ya tattaro kuma aka wallafa shi, cewa kimanin kudi wuri na gugar wuri har naira Biliyan Daya da aka ware don aikace aikacen maikatar dake kula da karatu a matakin farko a kasa baki daya wato (UBEC) a turance inda aka ware wan nan kudi don Gina makaranta irin ta zamani a yankin mazabar Bauchi ta kudu a majalisar tarayya amma kudin sunyi batar dabo, ko kuma an karkatar dasu wani wuri, inji rahoton.
Dan jarida Kuma mawallafin yace, ” misalin karfe 3:27 na yamman Talatar data wuce, Kanina ya Kira ni yake shaida min cewa wasu mutane da baisan ko au wane ne ba a cikin mota kirar Pijo 406 wadda an rufe lambar motan suka dira a gidansa, suna tambayan ina yake”
“Kanina ya kada baki ya ce musu nayi tafiya San nan suka furta ma kanin na cewa yasan abunda ya rubuta na batanci game da Yakubu Dogara kuwa? yace masu bashida masaniyar hakan” ya fada.
“Kana suka ce masa to na san da sani nayi nawa, saboda haka ma jira nasu”
Bugu da kari, Haruna yaci gaba da shaidawa, wan nan barazana tazo daidai bayan misalin awa guda da wasu gungun mutane masu suna (Dogara Digital Media Support) a turance, sukayi wani rubutu suka kuma raba dauke da yin Allah wadai da wan nan kafar watsa labarai ta yanar gizo watu (Wikki Times) data bankado wan nan badakala kudi kuma ta wallafa shi.
Ko a kwanan baya wan nan jarida ta (Wikki Times) tayi wani bincike mai zurfi kan wasu kudade da aka kashe ba bisa kai’da ba don tallafa ma talakawa masu fama da ciwon idanu domin basu taimako kyauta a Asibitin duba ido dake fadar Jihar Bauchi, wacce aka fi sani da suna (Makka Eye Clinic) dake kan Titin Kobi, inda ta kai ga hukumar gudanarwa ta Asibitin ta maka Jaridar a kotu da zargi yi mata kage, akan wan nan labari, inda kudade da yawa sukayi layar zana, a maimakon tallafa ma marasa galihu.
Kazalika, wata kungiya mai zaman kanta Mai suna (JCPJ) a turance mai bincike da bin kwakwafi, sun ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da ake muzguna ma Yan’jarida, da Kuma gudanar da aikinsu cikin rashin tabbas. #
