Rahotanni daga Fadar Shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa takwaransa na China Xi Jing Ping wasi?ar taya shi murnar cika shekara 100 da kafa jam’iyyar kwaminisanci da ke mulkin kasar.
Shugaban ya ce ?ar?ashin jagorancin shugaban na China, jam’iyyar ta samu nasarar ciyar da kasar gaba, kama daga kan ta fuskar tattalin arziki da walwalar ‘yan kasa.
Ya kuma yaba wa rawar da kasar ta taka wajen yaki da annobar korona a duniya a ?ankanin lokaci, harma ta farfado da tattalin arzikinta.
Buhari ya kuma yaba wa kakkarfar dangantakar da ke akwai tsakanin Najeriya da China, inda ya ce yana fatan za ta ci gaba da yau?a?a.
