‘Yan Bindiga Sun Yi Wasoson Mata Da Kananan Yara A Mahaifar Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle

IMG 20240421 WA0046

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da mutane 47 daga kauyen Danbaza a karamar hukumar Maradun mahaifar ?aramin ministan tsaro Bello Matawalle.

Wani mazaunin ?auyen, Abdul Danbaza, ya bayyana cewa ?an bindigar sun mamaye garin da misalin ?arfe 2:30 na dare ranar Laraba.

Ya shaidawa jaridar Leadership cewa maharan sun yi awon gaba da mutane 47 galibi mata da ?ananan yara zuwa cikin jeji.

Abdul ya ce ?an bindigar, wa?anda adadinsu ya kai 100 duka a kan babura ?auke da mugayen makamai sun bu?e wuta daga shiga kauyen.

Mutumin ya kara da cewa shi kansa yana cikin wa?anda maharan suka tattara suka tasa zuwa jeji amma a hanya ya samu ya ?uya a bayan wata itaciya, ya dawo gida. “Na taki sa’a da na kubuta daga hannun ‘yan fashin dajin da suka kai farmaki kauyenmu, amma abin takaici, mahaifina da wasu iyalina suna cikin wa?anda aka yi garkuwa da su.

A ?an kwanakin nan ?an bindiga sun yiwa mutane barazanar kai hari a kauyuka daban-daban da ke ?ar?ashin ?aramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Kauyukan da ?an bindiga suka kai hare-hare kwanan nan a ?aramar hukumar Maradun sun ha?a da Janbako, Goron Namaye, Kaya, da cikin garin Maradun.

Maradun dai ba tsaro kuma nan ne mahaifar karamin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle.

Wani bawan Allah mai suna Kabiru Abdullahi yace abun kunya ace garinsu ministan tsaro wai babu tsaro allah ya kyauta

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da harin da aka kai kauyen Danbaza da Maradun kuma ya yi alkawarin sakin bayanai nan gaba.

Related posts

Leave a Comment