Jirgin Shugaban Kasa: Za A Sayo Wa Tinubu Tsohon Jirgin Da Bankin Jamus Ya Kwace Hannun Wani Balarabe Mai Taurin Bashi

IMG 20240226 WA0252

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Jaridar PREMIUM TIMES na da tabbacin cewa shi ma Jirgin Shugaban ?asa da ake ta ha?ilon sayo wa Shugaban ?asa Bola Tinubu, tsoho ne, kuma daga wani Bankin Jamus za a sayi jirgin, wanda Bankin Jamus ya ?wace daga hannun wani attajirin Balarabe mai taurin-bashi.

Jirgin dai samfurin Airbus A330 ne da aka ?wace daga hannun Balaraben, wanda wani babban dillalin fetur ne da ya kasa biyan bankin wani bashin ma?udan ku?a?en da ya ke bin sa.

Sai dai jami’an Fadar Shugaban ?asa sun yi gum da bankin su, sun ?i cewa komai, dangane da shirin sayo jirgin na shugaban ?asa.

Amma kuma wannan jarida ta samu cikakken bayanin cewa gwamnatin tarayya tuni har ta za?o jirgin, amma a yanzu fa?i-tashin harha?a ku?in biya ake yi domin a tabbatar da shigar ciniki.

Shi dai jirgin, wani Balarabe ne ya bayar da shi ajiya ga Bankin Jamus, a matsayin kadara, lokacin da zai kar?i bashi a hannun bankin, domin ya sayi jirgin.

A irin wannan rance, daga lokacin da ka kar?i ku?in ka sayi jirgin, to bankin zai kar?e jirgin idan ka kasa biyan ku?in da ka ranta.

Majiyarmu ta ce jirgin dai ya zame wa Bankin Jamus ala?a?ai, bayan bankin ya rasa mai sayen sa, saboda tsadar sa.

A yanzu dai jirgin ya na hannun kamfanin L & L International LLC, wani kamfanin hada-hadar cinikin jirage da ke birnin Miami, Jihar Florida, a Amurka.

Kamfanin L & L ?in ne ke wa Bankin Jamus dillancin jirgin, ya na ?o?arin sayar wa gwamnatin Najeriya.

An ce jirgin dai irin na ?asaitattun mutane ne, wanda aka ?iyasta ku?in sa zai kai Dala miliyan 600.

“Ciniki ya kakare yayin da Gwamnatin Najeriya ta yi wa jirgin mugun-tayi kan Naira Dala miliyan 100,” haka wata majiya ta tabbatar wa jaridar nan, kuma babu ma tabbatacin kamfanin L & L zai amince da wannan mugun-tayi.

Wata majiya kuma ta shaida cewa, “idan har kamfanin L & L International ya sayar wa Najeriya jirgin a Dala miliyan 100, to Najeriya za ta iya sayar da shi nunki biyu na farashin da aka sayar mata da jirgin.

Kakakin Ya?a Labaran L & L International ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa ba shi da cikakken bayanin yadda cinikin jirgin ke tafiya, wanda jaridar ta gano cewa tuni har Najeriya ta taya jirgin, an ce albarka.

Wata majiya kuma a kamfanin AMAC Aerospace AG na ?asar Swiss, shi ne ke wa Najeriya dillacin sayo mata filin.

AMAAC Aerospace ne ke wa bargar Jiragen Fadar Shugaban ?asa garambawul tsawon shekaru da dama.

Majiya ta ce L & L ne ya samo labarin jirgin kuma ya labarta wa gwamnatin Najeriya, tare da bayar da shawarar ta sayi jirgin. Kamfanin ne ya tabbatar wa Najeriya cewa jirgin ranga?au yake, garau ba shi da wata matsalar komai.

PREMIUM TIMES ta tuntu?i Daraktan AMAC International, wato Daraktan Kula da Garambawul, Alexsis Ott, amma ya ?i ya ce komai. Ya ce shi ba ya tattauna batun hada-hadar ciniki da wanda ba shi da hannu a cikin cinikin da kuma ya ke so ya san abin da ake ciki.

Majiyoyi daga Fadar Shugaban ?asa sun bayyana cewa ana nan ana ta ha?ilon yadda za a ha?a ku?a?en sayo jirgin. Yayin da ita kuma gwamnati ta sa jiragen shugaban ?asa guda uku a kasuwa, amma kuma ta ha??a?e cewa ku?a?en da za a yi gwanjon jiragen uku ko ka?an ba za su kai ku?in sayen wancan dan?areren jirgi mallakar Bankin Jamus ba.

Related posts

Leave a Comment