Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida murnar zagayowar ranar haihuwarsa shekaru 80.
Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin babban mai ba shi shawara wajen yada labarai da hulda da jama’a, Malam Garba Shehu.
An ruwaito Garba Shehu yana cewa shugaba Muhammadu Buhari sun yi tarayya da Ibrahim Babangida wajen ganin kasa ta gyaru. Buhari ya yi kira ga Babangida da ire-irensa, su dage wajen ganin Najeriya ta yi nasarar kai ga ci.
“Muhammadu Buhari ya aika sakon taya murnarsa ga tsohon shugaba Ibrahim Babangida, ya na masa fatan tsawon rai da ?arin lafiya yayin da ya ke cika shekara 80.”
“Shugaban kasa Buhari ya ce a matsayinsu na tsofaffin sojojin yaki da suka yi ritaya, duk sun hadu a wajen fatan alheri da sha’awar ganin an samu hadin-kai a Najeriya.”
“Shugaban kasa Buhari ya na sa ran cewa manyan mutane irinsu tsohon shugaba Babangida da ire-irensa za su taimaka wajen taimakon kasar ga nasara, da cigaba.”
Rahoton ya ce Muhammadu Buhari ya shiga cikin sahun masu taya tsohon shugaban kasar na mulkin soja murnar kara shekarar da ya yi a ban kasa.
Tsohon Shugaban kasa Janar Babangida mai ritaya ya yi mulki na tsawon shekaru takwas tsakanin 1985 da 1993 bayan ya hambarar da gwamnatin Janar Buhari a wancan lokacin.
