Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar dokoki ta kasa ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin wata kotu da ta umarci ministan shari’a Abubakar Malami ya goge sashe na 84 (12) na sabuwar Dokar Za?en da Buhari ya sanyawa hannu.
Umarnin kotun na cire sashen da ya bukaci masu mukaman siyasa su ajiye mukamansu kafin neman wata takara ya janyo ce-ce-ku-ce kuma matakin na zuwa ne gabanin kakar zaben 2023.
Dama dai wasu ‘yan majalisar sun ce ba za ta sabu ba game da aiwatar da hukuncin kotun.
