Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ‘yan Bindiga masu garkuwa da mutane sun sace mutane da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.
Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci.
Ya bayyana cewa akwai motoci da dama wa?anda suna ajiye a kan ?angaren zuwa Kaduna da ?angaren dawowa da aka yi awon gaba da masu motocin.
Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ?umbin yawa sun isa wurin domin kai ?auki.
Dukkanin kokarin da aka yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura saboda bai ?aukar waya.
