Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam reshen Zariya jihar Kaduna ta maka Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa zarginsa da karkatar da ku?i naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta.
JNI ta ce an biya cekin ku?in ne ga kungiyar a matsayin diyyar kar?e filinta na Kwalejin Larabci domin aikin hanyar jirgin ?asa na Kaduna zuwa Zariya.
A karar da aka shigar a 25 ga Afrilu a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ?ungiyar da sakatare Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ?in.
Masu shigar da ?ara sun yi ikirarin cewa sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki.
