Tsohon mataimakin Shugaban ?asa Alhaji Atiku Abubakar ya bada tabbacin dawo da Najeriya cikin hayyacin ta idan ya yi nasarar zama shugaban ?asa a shekarar 2023.
Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyar PDP ta jihar Kaduna a ziyarar da ya kawo jihar domin neman goyon bayan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
“APC ta lalata Najeriya fiye da yadda ake zato, gyaruwar ?asar ya ta’allaka da samun jajirtaccen Mutum kamar ni, ina da tabbacin samun nasara idan aka tsayar dani takara”.
Tun farko da yake jawabi tsohon Gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin abin dogaro ga PDP a 2023 domin kai wa ga nasara.
