Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun sace wasu masallata a yayin da yan bindiga suka kai hari a wani masallaci a ?aramar hukumar Giwa ta jihar.
Wasu majiyoyi sun shaida cewa yan bindigan sun kai harin ne lokacin da mutanen ke sallar Ishai a ranar Alhamis.
A zantawar da aka yi dasu Mutanen garin sun tabbatarda harin, sun yi bayani kan barnar da yan bindigan suka yi inda suka ce “Sun zagaye masallacin suka sace mutane 14. Sun kuma sace shanu da ba a san adadin su ba a kauyen Tudun Amada duk a Giwa.”
Rahotanni sun bayyana cewar yan bindigan sun dade suna kokarin kai hari a jihar amma yan sakai suna hana su shiga garin.
Da ya ke magana a kan harin, wani mazaunin garin ya ce: “Yan bindigan sun raba kansu, wasu suna masallaci, wasu kuma suka rika bi gida-gida suka sace fiye da mata goma. “Wasu daga cikinsu kuma suna can suna sace dabobin gida kamar shanu, tumaki da awaji da suka haura daruruwa.”
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce zai bincike sannan zai bada bayani, bai bada bayanin ba har lokacin hada wannan rahoton.
