Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an bindigar da suka kai hari kan jirgin ?asan Abuja-Kaduna a watan Maris sun sake sako mutum hu?u uku daga cikin fasinjojin jirgin da suke ri?e da su.
Mai shiga tsakani a sasantawa tsakanin maharan da iyalan fasinjojin Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
“An saki mutane hu?un ne a ranar Juma’a da safe kuma sun zo har nan ofishina suka yi min godiyar shiga tsakani da na yi har maharan suka janye barazanar kashe su da suka yi a baya.
“Sun kuma ro?i dukkan masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya da ta tsaurara matakan ceto sauran fasinjojin da ke hannun maharan saboda halin abin tausayi da suka baro su a cikin dajin ,” a cewar Tukur Mamu.
Zuwa yanzu babu tabbaci kan ko an biya ku?in fansa kafin a sako mutanen, amma rahotanni na cewa na baya da aka sha saki sai da suka biya miliyoyin naira kafin su samu ‘yancinsu.
Daga cikin fasinjojin da aka saka ranar Juma’a har da dattijuwar da ta girmi dukkan fasinjojin, Mama Halimatu Atta mai shekara 90.
