Babbar Magana: Babban Dan Ganduje Ya Yi Karar Mahaifiyarshi A EFCC

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar babban ?an gwamnan Jihar mai suna Alhaji AbdulAziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Uwargidan Gwamnan Kano Hajiya Hafsat Goggo wajen EFCC

Hafsat Ganduje, Uwargidar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ta ki amsa gayyatar hukumar EFCC kan karar zargin cin Hanci da rashawa da ‘danta, AbdulAziz Ganduje, yai Mata,

An ruwaito cewa an gayyaci Hafsat Ganduje ranar Alhamis da ta gabata hedkwatar EFCC dake babban birnin tarayya Abuja.

Abdulazeez ya kai mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, kara wajen EFCC ne kan zarginta da amfani da karfin mulki wajen tarawa kanta dukiya.

A cewar majiyoyi da suka ga karar da Abdulazeez ya shigar, ya bayyana cewa wani mai gine-gine ya tuntubeshi don samun wasu filaye a Kano da dubban daloli da kuma N35m matsayin la’ada.

Mun samu labarin cewa Abdulaziz yace ya baiwa mahaifiyarsa kudin. Majiyar tace: “Bayan watanni uku, mutumin ya gano cewa filayen da yace a samar masa tuni an baiwa wasu mutane daban kuma ya bukaci a mayar masa da kudin da ya bayar.

Inda ita kuma ta yi kememe akan haka, lamarin da ya tu’azzara har ta kai ga matsayin da ?an nata ya dauki matakin gabatar da ita a gaban Hukumar EFCC.

Related posts

Leave a Comment