Rahotannin dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar manyan ‘yan Najeriya da dama ne suka halarci nadin sabon Sardaunan Dutse Alhaji Nasuru Haladu Danu da masarautar Dutse ta yi.
Mai girma mataimakin shugaban ?asa Alhaji Kashim Shettima da tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari da mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi da ministan zirga-zirgan jiragen sama Festus Kayemo duk sun halarci nadin.
Sauran manyan da suka halarci bikin nadin sun ha?a da mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar da mai martaba Sarkin Nasarawa Alhaji Ibrahim Usman Jibrin, sauran sun ha?a da shugaban gidan talabijin da rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi da sauran manyan ba?i da dama.
Na?in wanda mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Sanusi ya yi a fadar Masarautar ya bayyana Sabon Sardaunan a matsayin wani bango mai taimakon al’umma wanda nadin nashi ya zo akan lokaci.
Da yake jawabin godiya sabon Sardaunan na Dutse Alhaji Nasuru Haladu Danu ya gode wa mai martaba Sarkin Dutse da masarautar Dutse bisa ga nadin da aka yi mishi, inda ya bada tabbacin yin dukkanin mai yiwuwa wajen ciyar da masarautar Dutse da Jihar Jigawa gaba.
