Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiya ta duniya kuma jagoran yaki da rashawa na gaskiya.
Kungiyar masu binciken kwa-kwaf na Forensics na Najeriya watau Chartered Institute of Forensics and Certified Fraud Examiners of Nigeria (CIFCFEN) ne suka gabatar masa da wannan lambar yabo a Abuja.
A cewarsu, sun bashi ne don jinjinawa kokarin da yake yi wajen yaki da rashawa da kuma jajircewarsa wajen yiwa ‘yan Najeriya aiki kan gaskiya da ri?on Amana.
A jawabin da mai magana da yawun Buhari, Mr Femi Adesina, ya fitar, ya ce Shugaban majalisar amintattun CIFCFEN, Dr Iliyasu Gashinbaki, ne ya gabatar da lambar yabon ranar Talata a Abuja.
A cewarsa, babu wanda ake ba wannan lambar yabon illa shugabannin kasashen Afrika masu hali na kwarai. Yace Shugaba Buhari ne shugaban kasa a nahiyar Afrika na farko da aka ba wannan lambar yabo.
A jawabin shugaba Buhari ya bayyana cewar: “Wannan karramawa na kara min karfin gwiwan cewa mu ‘yan kasar nan zamu iya abinda ya dace da kuma kwaikwayon halayen magabatanmu na ?warai”.
Buhari ya jinjinawa mambobin kungiyar bisa kokarin da suke wajen taimakawa kungiyoyin yaki da rashawa irinsu EFCC, CCB, ICPC da hukumar yan sanda, sannan ya yi musu alkawarin sanya hannu kan dokar majalisa dake kan teburinsa wacce ke tabbatar da kungiyarsu a hukunmance.
