An kira yi al’umma Musulmi da su mai da hankali wajen ba ‘ya’yan su ilimin Al-qur ani mai girma domin samar musu nagartacecen ilimin addinin musulunci.
Mai martaba Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa ne yayi wannŕn kira a lokacin da yake jawabi a wurin bu?e gasar karatun Al-qur ani mai girma na kasa wanda kungiyar shirya gasar Alqur’ani na ?alibai Mata zalla (RABIDA) ta shirya a Yola.
Lamido wanda hakimim cikin garin Yola kuma Cika Soron Adamawa wato Muhammed Ahmed Mustafa ya wakillta yace ba yara ilimin addini tun suna kanana yana da matukar muhimmanci wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban addinin musulunci yadda ya kamata.
Lamido ya kuma shawarci Al’umma Musulmai da su kasance masu sanya tsoron Allah madaukakin sarki a zukatansu a koda yaushe domin samun tsira ranan gobe kiyama.
Shima tun da farko a jawabinsa shugaban kwamitin shirya gasar kuma shugaban majalisar addinin musulunci a jihar Adamawa Malam Gambo Jika ya nuna farin cikinsŕ dangane irin goyon baya da Al’umma Musulmai suka bayar domin ganin an gudanar da gasar cikin lumana.
A nata jawabi Amiran Rabida a jihar Adamawa kiran iyaye mata tayi da su mai da hankali wajen ba yaransu tarbiya ta gari musammanma mata kasancewarsu iyayen Al’umma.
Za a dauki a kalla mako daya ana gudanar da gasan wanda zai gudana a makaranta kwalejin ilimi ta tarayya dake Yola, wanda kuma ana saran daukacin jihohi talatin da shida harda birnin tarayya Abuja zasu halarci gasar karatun Al Qurani mai girma.
