Rahotanni daga birnin London na kasar Birtaniya na bayyana cewar Babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya kawai dai ana cigaba da duba lafiyarsa ne a Landan.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga yan Arewa mambobin majalisar wakilan tarayya da suka kai masa ziyara ranar Juma’a.
Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne ya kwashe watanni uku yanzu a birni Landan tun bayan da aka yi masa aikin tiyata a gwiwa. Amma yanzu yace kawai yana hutawa ne sannan ana duba lafiyarsa lokaci bayan lokaci.
A jawabin da yayi musu yana mai sanye da Kaftani da jar hula, Tinubu yace: “Saboda Allah ina sanar da mutane irinku, ina cikin koshin lafiya. Kawai duba lafiyar ne yayi tsanani.”
Yan majalisar wakilan Najeriya na arewacin kasar nan sun samu jagorancin mataimakin kakakin majalisa, Ahmed Idris Wase inda suka ziyarci jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a London ranar cikar Najeriya shekaru sittin da daya da samun ‘yancin kai.
‘Yan majalisar wakilan sun hada da na yankin arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
