Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Kwadago Ta Gudanar Da Zanga-Zanga

Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewa masu zanga-zangar goyon bayan kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU bisa ga umarnin uwar ?ungiyar ?wadago ta ?asa NLC sun mamaye ofishin gwamnatin jihar ta Legas.

Rahotanni na cewa tun da misalin karfe 7:00 na safiya ne daruruwan masu zanga-zangar suka taru a birnin Ikeja, inda suka cika babban titin birnin, suka kuma nufi gidan gwamnatin jihar

Zanga-zangar dai ta janyo cinkoson ababen hawa a jihar wacce ke da tarin ababen hawa.

Haka ma a sauran jihohin kasar an samu fitowar daruruwan masu zanga-zangar, kamar yadda Uwar kungiyar ta kasa ta umarci rassanta na jihohi da su fito domin gudanar da zanga-zangar goyon bayan ASUU.

Related posts

Leave a Comment