Talauci Da Fatara Na Fuskantar Duniya – Hukumar Bada Lamuni

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ?asar Amurka na bayyana cewa hukumar lamuni ta duniya IMF ta yi gargadin cewa duniya za ta iya sake shiga cikin mawuyacin hali na koma bayan tattalin arziki mafi muni, idan har ba a shawo kan illolin yakin Ukraine da hauhawar farashin kayayyaki ba.

A sabon hasashen tattalin arzikin duniya, hukumar ta yi hasashen cewa, za a samu tangardar ci gaban tattalin arziki da sama da kashi uku cikin dari a bana, kuma zai kara raguwa da kusan kashi uku zuwa badi.

Babban masanin tattalin arzikin hukumar ya ce yawan kudin ruwa da ake karawa don magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, karin illa ne ga matsalar.

Pierre-Olivier Gourinchas ya ce tattalin arzikin China da Amurka da Turai na tsaye ne ba wani motsi, kuma akwai rikicin bashi da ya dabaibaye kasashe masu tasowa.

Related posts

Leave a Comment