Yajin Aiki: Kotu Ta Dage Saurarar Karar Da Gwamnatin Tarayya Ta Kai ASUU

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun masana’antu a ranar Litinin ta dage sauraron sharia’a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.

Mai shari’a Polycarp Hamman ya dage sauraron shari’ar ne saboda a bai wa gwamnatin tarayya mika dukkan takardun da suka dace don karar, wadda ke ?alubalantar matakin da kungiyar malaman ta ?auka na kassara ilimi a ?asar.

Channels TV ta rahoto. KARA KARANTA WANNAN Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari’a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta garzaya gaban kotun masa’antu ta kasa dake zama a Abuja inda take bukatar a umarci kungiyar malamai masu koyarwa ta jami’o’i, ASUU, da su koma bakin aikinsu a yayin da ake kokarin shawo kan rashin jituwar dake tsakaninsu.

Related posts

Leave a Comment