Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce Har yanzu ba ta raba mu?amai a majalisa ta 10 ba kamar yadda ake ya?a wa a shafukan sada zumunta.
Jam’iyyar ta ce zuwa yanzu ba ta ke?e wani mu?ami zuwa ga wani shiyya na ?asar cikin shiyoyyi shida da tae da su, musamman ma na majalisar tarayya ta 10 da ake shirin kafawa.
Cikin wata sanarwa da APC ta fitar jiya Alhamis wanda ya samu sa hannun sakataren hul?a na ?asa Felix Morka, ta ce bayanin da ake ya?a ba daga gare ta ya fito ba, don haka ta ce mutane su yi wasi da shi.
APC ta ce za ta fitar da sanarwa kan matakin idan har bukatar hakan ta taso.
